Ministan tsaron Isra’ila Yoav Gallant ya yi umarnin a “yi wa Zirin Gaza ƙawanya, babu shigar abinci, babu wuta sannan ba man fetur”.
A wani mataki na matashiya, Isra’ila ce ke da iko da sararin samaniyar Gaza da kuma hanyoyin ruwansa, sannan ta sanya takunkumai a kan wane ne da kuma me za a iya shiga da shi ta kan iyakar yankin.
Haka kuma a ɗaya ɓangaren, inda Masar ke iko da iyakar Gazan, ita ma tana lura da wane ne zai shiga ko kuma ya fita daga yankin.