Iran ta zama ƙasar musulmi ta farko da ta harba satellite ɗinta a duniyar Mass

0
445
Iran ta zama ƙasar musulmi ta farko da ta harba satellite ɗinta a duniyar Mass

Iran ta zama ƙasar musulmi ta farko da ta harba satellite ɗinta a duniyar Mass

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta zama ƙasar musulmi ta farko a duniya da ta samu nasarar harba Setilite ɗinta a sararin samaniyar duniyar Mass, wanda ke ɗauke da Internet ɗinta mai zaman kansa.

Wannan babban nasara da ƙasar ta Iran ta samu dai ya sa ta shiga cikin jerin ƙasashe 7 kacal da suka iya mallakar setilite ɗinsu. Yanzu dai ƙasashen Turai, irinsu Amurka da Isra’ila ba za su iya samun damar yiwa ƙasar Iran leƙen asiri ba, saboda za ta daina amfani da fasahar GPS mallakar ƙasar Amurka, wadda ƙasashen Turai har da Isra’ila da sauran ƙasashen duniya ke amfani da a shi.

KU KUMA KARANTA: Sayyid Khamene’i ya sake naɗa manyan Malamai 3 a majalisar tsaron Iran

Yin amfani da setilite ɗin GPS na ƙasar Amurka da Iran ke yi ne ya sa Amurka ke iya samun cikakken iko da sararin samaniyar Iran, inda ita kuma Amurka ke ba wa Isra’ila bayanan sirrin ƙasar ta Iran.

KU KUMA KARANTA: Za mu ci gaba da haɓaka Uranium a ƙasar mu — Shugaba Pezeshkian na Iran 

Ga jerin ƙasashen duniya 8 da suke amfani da setilite ɗin kansu:

1. Rasha

2. Amurka

3. Faransa

4. Burtaniya

5. China

6. North Korea

Sai kuma Iran wadda ta samu nasarar harba nata a yammacin ranar Talatar nan.

Bayan samun nasara, Iran ta ce a halin yanzu idan sauran ƙasashen musulman duniya suna son daina amfani da GPS na ƙasar Amurka ko Baidu na ƙasar China su dawo amfani da na ƙasar Iran, to kyauta 0.00 Charges Iran za ta ba su damar yin hakan, amma duk wata ƙasar da ba ta musulmai ba sai sun biya kuɗi, amma za ta musu rangwame sosai.

Leave a Reply