No menu items!

Sample Page Title

Date:

Hukumar kula da gasar firimiya ta Nigeria a ranar Litinin ta ci tarar Kano Pillars kuɗi har Naira miliyan ɗaya, sakamakon kutsen da magoya bayansu suka yi a filin wasa, a wasan da suka fafata da Rivers United.

An tabbatar da cewa magoya bayan ƙungiyar Kano Pillars sun ƙetara shingen filin wasa domin murnar cin ƙwallon da suka yi a minti na 92 ​​a karawar da suka yi a filin wasa na Sani Abacha.

Bayan nazarin rahotanni daga jami’an wasan, hukumar kula da gasar Firimiya ta Najeriya, NPFL ta tuhumi kulob ɗin da laifin karya doka mai lamba B13.18. Ta hukumar.

Don haka an umurci kulob ɗin da ya biya tarar cikin kwana 14, kuma ya ja kunne kan hakan, wanda gaza yin hakan zai zamo tamkar ci gaba da saɓa wa dokokin hukumar ta NPFL.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...