Hukumar Tattare Haraji ta Jihar Kano ta kori daraktoci takwas

0
129

Hukumar tara haraji ta jihar Kano (KIRS) ta sanar da korar daraktoci 8 daga muƙamansu, inda ta umarce su da su miƙa duk wani aiki da muƙamai ga mataimakan su.

Shugaban hukumar tattara kuɗaɗen shiga ta jihar Kano (KIRS), Alhaji Sani Abdulkadir Dambo ne ya sanar da hakan a wata sanarwa daga ofishin sa.

Ya ƙara da cewa, “A ci gaba da ƙoƙarin da ake yi na cimma manufofin gwamnati mai ci, an umurce ni da in sanar da ku cewa an sauke daraktocin, kuma za su miƙa takardun aikinsu ga mataimakansu nan take.

KU KUMA KARANTA: An kori ‘yan sanda biyu daga aiki bayan samun su da yin fashi da makami

A cewar sanarwar, daraktocin sassan da abin ya shafa sun haɗa da: Darakta Muhammad Kabir Umar; Daraktan Ma’aikata, Kabiru Magaji; Daraktan Kasuwanci Ibrahim Sammani; Aminu Umar Kawu, Daraktan Muhd Auwal Abdullahi, Daraktan Binciken Haraji

Ta ƙara da cewa sauran daraktoci sun haɗa da Abubakar Garba Yusuf, Daraktan ICT, Hamisu Ado Magaji, Daraktan PAYE, da Bashir Yusuf Madobi, Daraktan Legal & Enforcement.

Leave a Reply