Hukumar NSCDC ta kama mutane 7 da ake zargi da sace murafan kwalbati

0
31
Hukumar NSCDC ta kama mutane 7 da ake zargi da sace murafan kwalbati

Hukumar NSCDC ta kama mutane 7 da ake zargi da sace murafan kwalbati

Hukumar tsaro ta NSCDC, a babban birnin tarayya, Abuja, za ta gurfanar da wasu mutane bakwai da ake zargi da lalata muhimman ababen more rayuwa a birnin.

Kwamandan rundunar na Abuja, Olusola Odumosu, ya bayyana haka a lokacin da yake baje kolin kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin a hedikwatar rundunar da ke Abuja.

Odumosu ya ce an kama biyar daga cikin waɗanda ake zargi da aikata laifin ne yayin da suke cire murafan kwalbatin magudanar ruwa da igiyoyin wutar lantarki a birnin.

KU KUMA KARANTA: ’Yan bindiga a Zamfara sun sace fasinjoji, sun ƙone mota

Ya ce, an kama mutanen biyar ne da tsakar dare, wadanda shekarunsu ke tsakanin shekaru 19 zuwa 24.

Leave a Reply