Hukumar Kwastam da NAFDAC sun kama miyagun ƙwayoyi da kuɗinsu ya haura Miliyan 150

0
182
Hukumar Kwastam da NAFDAC sun kama miyagun ƙwayoyi da kuɗinsu ya haura Miliyan 150

Hukumar Kwastam da NAFDAC sun kama miyagun ƙwayoyi da kuɗinsu ya haura Miliyan 150

Daga Jameel Lawan Yakasai

Hukumar hana fasa ƙwauri (Kwastam) ta miƙa wa hukumar kula da ingancin abinci da magunguna NAFDAC kwayar Tramadol sama da dubu 400 da 91, wadda kuɗinta ya haura Naira miliyan 150 da dubu 360.

Shugaban hukumar COSTOM mai kula da jihohin Kano da Jigawa, Abubakar Dalhatu ne ya miƙa ƙwayoyin a ofishin hukumar na Kano a rana Litinin, bayan jami’ansu sun samu nasarar kama su a kan iyakar shigowa Gumel a jihar Jigawa a wata mota ƙirar JEEP.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta buƙaci a zartar da hukuncin kisa kan masu fataucin ƙwaya

Da yake karbar ƙwayoyin Tiramadol din, jami’in hukumar NAFDAC, Kasim Idris Ibrahim, ya ce a binciken da suka gudanar ya gano cewa, an shigo da kayan ne daga kasashen ketare, waɗanda suma suka haramta yin amfani da da su.

Ya tabbatar da cewa nan gaba kaɗan za su sanar da lalata wadannan miyagun kwayoyi.

Leave a Reply