Tinubu ya amince da mayar da Kwalejin Fasaha ta Kabo dake Kano zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha
Daga Jameel Lawan Yakasai
Mataimakin shugaban Majalisar dattijai, Sanata Barau Jibrin, ne ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook, inda yace wannan mataki ya nuna irin jajircewar Shugaban Ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, wajen inganta damar samun ilimi a matakin gaba da sakandare da kuma ci gaban ƙasa ta hanyar bai wa matasa ƙwarewar da ake bukata a wannan zamani.
“Takardar amincewa daga Shugaban Ƙasa zuwa ga Majalisar Dattawa, wadda ta shafi kudirin da na dau nauyinsa, an karanta ta a zauren Majalisar Dattawa yayin zaman yau, karkashin jagorancin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Obot Akpabio.”
“Kamar yadda muka sani, matasa su ne ginshikin cigaban kowace al’umma. Sauya wannan makaranta zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ya yi daidai da matakan da ake bi a duniya wajen bunkasa ilimi da ci gaba.”
KU KUMA KARANTA: Abubuwa 10 da za su iya faruwa idan Tinubu ya zarce a wa’adi na biyu – Hasashen KY Tebo
“Muna da yawan matasa a Najeriya, kuma a duniyar yau, cigaban ƙarfin ɗan Adam na da matuƙar muhimmanci wajen haɓaka tattalin arziki da ci gaban kasa.”
“A duniya, fannoni kamar ICT, fasahar kere-kere (AI), na’urori masu sarrafa kansu (robotics), tsaro ta yanar gizo (cybersecurity) da makamantansu suna cikin abin da ake mai da hankali a kai. Ta irin wannan jami’a ne za mu horar da matasanmu a wadannan fannonin.”
“Ina taya shugabanci, ma’aikata, dalibai da al’ummomin da ke kewaye da Federal Polytechnic Kabo murna bisa wannan babban ci gaba.” – inji Barau Jibrin