Hukumar KAROTA ta cafke wasu matasa da tarin kayan maye da makamai a Kano

0
218

Daga Shafaatu Dauda, Kano

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA, ta ce jami’anta sun cafke wasu matasa da ake zargin ɓata gari ne.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta Nabilusi Abubakar Ƙofar Na’isa ya raba wa manema labarai a yau Talata.

Sanarwar ta ce, jami’an sintiri na hukumar ne suka samu nasarar cafke matasan da daddare a ƙarƙashin gadar Dangi.

Haka kuma hukumar ta ce, guda daga cikin jami’anta da suka cafke waɗanda ake zargin, mai suna Mas’ud Ya’u Yusuf ya ce, sun kama su ne lokacin da suka iske su suna kwance a ƙarƙashin gadar inda suka same su da nau’ikan kayan shaye-shaye da makamai.

Sanarwar ta ƙara da cewa waɗanda ake zargin sun faɗa wa Hukumar cewa kwanansu huɗu da shigowa garin Kano Daga jihohin katsina da Zamfara.

Hukumar tace, bayan kammala bincike ta mika matasan ofishin yan sanda na Yar akwa domin fadada bincike tare da daukar mataki na gaba.

Sanarwar ta ƙara da cewa, shugaban hukumar ta KAROTA Baffa Babba Dan Agundi ya yaba da ƙoƙarin jami’an, sannan ya yi kira ga daukacin al’umma da su ci gaba da kai rahoton duk wani motsi na waɗansu mutane da ba su yarda da su ba domin tabbatar da tsaron unguwanni da ma Jihar Kano baki daya.

Leave a Reply