Hukumar KAROTA a Kano ta gargaɗi masu kai wa jami’anta farmaki
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Hukumar Kula da Zirgar-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano, KAROTA, ta gargaɗi direbobin da ke kai wa jami’anta farmaki yayin gudanar da ayyukansu akan tituna.
KU KUMA KARANTA:Jami’an tsaro sun hana mu gawarwakin ‘yan’uwanmu da Sojoji suka kashe a Abuja – Mabiya Shi’a
Shugaban Hukumar, Injiniya Faisal Mahmud Kabir, ya yi wannan gargaɗin a cikin sanarwa da Kakakin Hukumar, Abubakar Ibrahim Sharaɗa ya aike wa tashar Dala FM Kano, a ranar Laraba, 9 ga watan Afrilun 2025.
Sanarwar na zuwa ne bayan wani farmaki da wasu mutane cikin baburin Adai-daita Sahu suka kai wa jami’an na KAROTA yayin da suke tsaka da aikinsu a kan hanyar zuwa Gidan Zoo .