Jami’an tsaro sun hana mu gawarwakin ‘yan’uwanmu da Sojoji suka kashe a Abuja – Mabiya Shi’a

0
202
Jami'an tsaro sun hana mu gawarwakin 'yan'uwanmu da Sojoji suka kashe a Abuja - Mabiya Shi'a

Jami’an tsaro sun hana mu gawarwakin ‘yan’uwanmu da Sojoji suka kashe a Abuja – Mabiya Shi’a

Daga Ibraheem El-Tafseer

‘Yan Shi’a almajiran Shaikh Zakzaky sun zargi jami’an tsaro kan hana su gawarwakin ‘yan’uwansu 26 da Sojoji suka kashe, tare da tsare musu mutane 274.

Harkar Musulunci wanda Shaikh Ibraheem Zakzaky yake ma jagoranci ta ƙira ga gamayyar jami’an tsaron Najeriya kan kashe mata kimanin mutane ashirin da shida tare da tsare aƙalla mutane ɗari biyu da saba’in da huɗu yayin gudanar da jerin gwanon tunawa da Palasɗinawa da suka yi a Abuja makon ƙarshe na watan Ramadana.

‘Yan Shi’ar dai sun bayyana yadda aka kama mutanen nasu, inda aka ɗauki wasu cikin jini daga wajen Muzaharar, ciki kuwa har da yara masu ƙananan shekaru kamar yanda suka bayyana wanda adadinsu ya kai mutum sittin tare kuma da masu raunuka akalla mutum 11.

Hakan na zuwa ne a wani takardar nemana labarai da kungiyar ta Harkar Musulunci karkashin jagorancin Shaikh Ibrahim Zakzaky suka fitar.

KU KUMA KARANTA:Shaikh Zakzaky ya raba abinci don Iftar: ‘Iftar Hadiyya’ (Hotuna)

Takardar wacce ɗaya daga cikin jiga-jigan Ƙungiyar, Sheikh Sidi Munnir Mainasara ya sa ma hannu ta bayyana cewa: “Abunda muka sani shine a ranar Juma’a wanda yayi dai dai da 28 ga wayan mayun 2025 da misalin karfe 2 na rana, sojojin da suke Gadin Shugaban kasa wanda ake kira da ‘Guards Brigade’ sun tare Muzahararmu ta Quds na shekara 2025 a Abuja, a daidai masallacin Usman bn Affan dake titin Aminu Kano, Abuja, Sojojin sun kashe kimanin mutane 26 sannan sun kama mutane 274, ciki harda yara masu ƙananan shekaru su 60 da masu raunuka da har yanzu ba’a musu magani ba su 11.

“Kuma har zuwa yanzu da nake wannan maganan Sojoji da yan sanda basu sake mana gawarwakin yan Uwanmu da suka kashe ɗin ba.

“Ita dai Muzaharar Quds Shugaban Gwagwarmaya na Iran Imam Khűmeyn ne ya assasa ta a shekarar 1979, cikin lumana ake gudanarwa a sama da ƙasashen duniya 80.

“Muzahara ce ta nuna goyon baya ga mutanen kasar Palasɗinu da aka kashewa, Inji Sheikh Sidi Munnir Mainasara

A karshe dai sun nemi da a gaggauta Sakin gawarwakin yan Uwan nasu tare da wadanda aka kama ake tsare dasu ba bisa ka’ida ba kamar yanda suka bayyana.

Leave a Reply