Hukumar FRSC ta ƙwato motoci 385 da aka sace ta hanyar sabon tsarin tantancewa

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC), ta ce ta ƙwato motoci sama da 385 da aka sace tun bayan ƙaddamar da shirin tantance ababen hawa na ƙasa (NVIS).

Jami’in hulɗa da jama’a na FRSC, Bisi Kazeem ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa ranar Litinin a Abuja.

A cewarsa, hukumar ta FRSC ta samu gagarumar nasara tare da ɓullo da shirin NVIS a fannin tattara bayanan sirri da musayar bayanai.

Ya ce hakan ya taimaka wajen ƙwato motocin da aka sace, da kuma “samar da hukumomin tsaro da isassun bayanan sirri don hanzarta bin diddigin masu aikata laifuka”.

“Don haka yana da matuƙar muhimmanci a sanar da jama’a cewa a cikin shekaru 10 da suka gabata kaɗai, hukumar FRSC ta ƙwato motoci sama da 385 da aka sace a Najeriya.

KU KUMA KARANTA: Amfani da tayoyin jabu da gudun wuce ƙa’ida ne ke kashe yawancin masu ababen hawa – FRSC

Mista Kazeem ya ƙara da cewa “Wannan ya faru ne ta hanyar kayan aikin NVIS da sauran dabarun aiki,” in ji Mista Kazeem.

Ya ce daga cikin motocin da aka ƙwato kwanan nan akwai Tirela mai lamba BEN 477 XC da aka sace.

Mista Kazeem ya ce motar ta lalace ne a mahaɗar jami’ar Babcock da ke garin Ilishan a ƙasar Benin kuma hukumar ta FRSC ta ja ta domin tabbatar da zirga-zirgar ababen hawa.

“Daga baya an gano ta ta hanyar bincike mai zurfi cewa motar sata ce,” in ji shi.


Comments

One response to “Hukumar FRSC ta ƙwato motoci 385 da aka sace ta hanyar sabon tsarin tantancewa”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Hukumar FRSC ta ƙwato motoci 385 da aka sace ta hanyar sabon tsarin tantancewa […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *