Hukumar EFCC ta saki tsohon gwamnan Benuwe Ortom, bayan shafe sa’o’i tara a hanunsu

0
302

A ranar talata ne Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC), ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, na tsawon sa’o’i tara kafin daga bisani a sake shi.

Ortom ya isa harabar hedikwatar hukumar, Makurɗi, da ƙarfe 10 na safe kuma ya bar wurin da misalin ƙarfe 7:00 na yamma.

Da yake mayar da martani, mai taimaka wa Mista Ortom kan harkokin yaɗa labarai, Terver Akase, ya ce saɓanin yadda ake zarge-zarge a wasu sassan kafafen yaɗa labarai, ba a kama tsohon gwamnan ba sai dai ya mutunta gayyatar da hukumar ta yi masa.

“Ba a kama Ortom ba kuma ba a tsare shi a hedikwatar EFCC da ke Makurɗi, ba” in ji Mista Akase.

KU KUMA KARANTA: EFCC ta kama ma’aikatan FMC 50 bisa zargin zamba ta intanet a jihohin Ogun da Oyo

A cewarsa, tsohon gwamnan ba shi da wani abin ɓoyewa, inda ya ƙara
da cewa zai kasance a ko da yaushe domin amsa tambayoyi daga hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

“Ortom ba shi da wani abin da zai ɓoye game da shugabancinsa a jihar,” in ji Mista Akase.

Leave a Reply