Hukumar EFCC ta kama mutane 33 da ake zargi da damfara ta yanar gizo

2
455

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) a ƙoƙarinta na daƙile yawaitar laifukan da suka shafi zamba ta yanar
gizo a tsakanin matasa, ta kama wasu mutane 33 da ake zargi da aikata laifuka ta yanar gizo a Ilorin jihar Kwara da Maiduguri jihar Borno.

Kakakin Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Ta’annati, (EFCC), Wilson Uwujaren, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Abuja.

A cewarsa, an kama 20 daga cikin waɗanda ake zargin ne a Ilorin, yayin da sauran 13 da ake zargin an kama su ne a Maiduguri.

KU KUMA KARANTA: Hukumar EFCC ta gurfanar da ma’aikatan bankin UBA biyu, bisa laifin satar naira miliyan 20

“Waɗanda aka kama a Ilorin sun haɗa da Habeeb Abubakar, Abiola Abiodun, Atitebi Samuel, Emmanuel Oborirhwoho, John Adamson, Mayowa Akinola Victor, Oluwafemi Ola, Abdullahi Isiak, Orji Roland, Martinson Adegboyega da Kolawole Temidayo.

“Sauran su ne Orimadegun Ishola, Tijani Quadri, Adebisi Kazeem, Umar Abdulkareem, Adebisi Teslim, Okunlola Ayomide, Quadri Lekan, Ukueni Great da Adeyeye Usman.

“An kama su ne a Egbejila, titin filin jirgin sama da kuma Offa Garage a Ilorin bayan samun sahihan bayanan sirri da ake zarginsu da aikatawa,” in ji shi.

Ya ce kayayyakin da aka ƙwato daga wajensu sun haɗa da nau’ukan wayoyi daban-daban, kwamfutoci da manyan motoci.

Uwujaren ya ce waɗanda aka kama a Maiduguri sun haɗa da Wilson Akpotaire, Adamu Mohammed, Adetoro Opeyemi, Musbahudeen Opeyemi da Bolanle Alhassan-Olaitan.

“Sauran su ne Joshua Ohaneye, Yusuf Philip, Mohammed Tijjani, Ahmed Andrew, Sangari Amilah, Maina Matakun, Oshalaiye Augustine da Kefas Victor.

“An tsince su ne a kusa da Titin Tashan Bama, Maiduguri, Jihar Borno, a ranar Litinin, 5 ga watan Yuni.

“Abubuwan da aka gano sun haɗa da nau’ikan wayoyin hannu daban-daban kuma waɗanda ake zargin za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike,” inji shi.

2 COMMENTS

Leave a Reply