Jami’an hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) sun kama wasu mutane 28 da ake zargi da damfarar yanar gizo a wani samame da suka kai a Inugu.
Kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja waɗanda ake zargin, a cewar sa sune: Godwin Ogbonna, Bright Chidozie, Chukwuebuka Ugwu, Ifesi Isaac, Collins Nnachi, Micheal Nnamdi, Ikechukwu Anya, Nneji Onyebuchi, Nwali Chukwudi da Godwin Okwuchi Promise “Sauran sun haɗa da Chijioke Henry, Chinwetalu Harrison, Somadina James, Ejike Ezeoha, Seth Onodika, Akuh Stanley, Emmanuel Opara, Nonso Martin, Ugochukwu Ibeh da Ikenna Okonkwo. “Haka kuma an kama su: Kenechukwu Barry, Ibe Chisom, Felix Nwaeze, Daniel John, Somtochukwu Zadok, Ugochukwu Amoke da Chukwudi Charles,” inji shi.
KU KUMA KARANTA: Hukumar EFCC ta kama maɓoyar ‘Yahoo-Yahoo’ a Benuwe, ta kama mutane 14 da ake zargi
A cewarsa, kayayyakin da aka ƙwato daga wajensu sun haɗa da wasu manyan motoci guda 9, wayoyin hannu 44, kwamfutoci bakwai da fasfo na ƙasa da ƙasa ɗaya.
Ya ce waɗanda ake zargin sun yi maganganu masu amfani kuma za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike.
[…] KU KUMA KARANTA: Hukumar EFCC a Inugu, ta kama mutane 28 da ake zargi da damfara ta yanar gizo […]