Hukuma tayi ram da Alasan Ado Doguwa, bisa tuhumar kisan kai

Ana dai zargin Alasan Ado Doguwan ne da amfani da bindiga ya harbi mutane, inda wasu da yawa suka rasa rayukansu har lahira, wasu kuma suka jikkata da munanan raunuka da ƙuna a balahirar zaɓen da ta gabata.

KU KUMA KARANTA: Hukumar DSS ta ƙwato makamai a jihohi daban-daban biyo bayan hare-haren siyasa a Kano

Alasan ɗin dai da ma an san shi da munanan kalamai na tunzuri da rashin mutunci. Ya yi zage-zage da yawa a baya, kuma ya nuna cewa duk wanda bai zaɓe su ba sai ya ci ubansa.

Ana dai zargin Alasan ɗin da kisan rayuka tare da ƙone ofishin jam’iyyar NNPP da ke Doguwa.

Cikakken bayani na zuwa nan gaba


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *