Hisbah za ta aurar da tubabbun ‘yan daba a Kano
Daga Jameel Lawan Yakasai
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce za ta duba yiwuwar baiwa tubabbun ƴandaba da gwamnati ta yafewa gurabe a shirin ta na auren gata.
Kwamandan Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Daurawa ne ya faɗi hakan yayin taron yaye tubabbun ƴandaba 718 da gwamnati ta yafewa, ƙarƙashin shirin “Safe Corridor”, wanda ya gudana a shelkwatar ƴansanda ta Kano a jiya Laraba.

Ya ce idan su ka tabbatar da shiryuwar su, a shirye Hisbah ta ke ta baiwa mai buƙata gurbin auren gata din don ƙara samun mutuwa da kintsuwa a rayuwar su.
KU KUMA KARANTA: Hisbah a Kano ta ja kunnen Amare da su daina zaman Majalisa idan mazajen su sun fita
Daurawa, ya roƙi waɗanda suka amfana da su ƙarfafa sauran waɗanda har yanzu ba su miƙa wuya ba da su yi hakan.
Ya ƙara da cewa, ya kamata waɗanda suka amfana da shirin na yafiya da su rika bayar da sahihan bayanai ga hukumomin tsaro waɗanda za su kai ga cafke masu fataucin miyagun ƙwayoyi a cikin jihar.









