Hisbah a Kano ta ja kunnen Amare da su daina zaman Majalisa idan mazajen su sun fita

0
48
Hisbah a Kano ta ja kunnen Amare da su daina zaman Majalisa idan mazajen su sun fita

Hisbah a Kano ta ja kunnen Amare da su daina zaman Majalisa idan mazajen su sun fita

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Hukumar da ke Umarni da kyakkyawan aiki, da hani da mummunan aiki ta Hisbah ta jihar Kano ta gargaɗi sabbin Amare su guji ɗabiʼar zaman majalisa da su ke yi da zarar mazajensu sun fita aiki musamman a sabbin unguwanni.

Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar Dr. Mujahid Aminuddeen ne ya bayyana hakan ga Jaridar Neptune Prime a Kano

KU KUMA KARANTA:Ƙungiyar kiristoci a Kaduna ta nemi a bawa ‘ya’yanta aiki a hukumar Hisbah

Ya ce, zuwa yanzu Hisbah ta karbi korafe-korafe daga unguwanni mabanbanta kan wannan dabiʼar, kuma tuni suka shiga nazari don daukar matakin da ya dace.

Dr. Mujahid ya kuma yi kira ga magidanta da su sanya ido sannan su tsawatarwa matansu.

Leave a Reply