Hatsarin mota ya ci rayukan ‘yan sanda uku a Kaduna

Wasu ‘yan sanda uku sun rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a garin Kidanda da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.

‘Yan sandan na tafiya ne zuwa karamar hukumar Giwa bayan halartar bikin Hawan Dauche a birnin Zariya a ranar Lahadi, inda hatsarin ya afku da misalin karfe 9 na dare.

KU KUMA KARANTA: Mutum bakwai sun ƙone ƙurmus, 14 sun jikkata a hatsarin mota daga Legas zuwa Ibadan

An ruwaito cewa ɗaya daga cikin tayoyin motar ‘yan sanda ne ta fashe a kauyen Sako, a Kidanda, wanda kuma ya yi sanadiyar mutuwar jami’an guda uku.

Wasu uku kuma sun jikkata, inda aka garzaya da su asibiti domin kula da lafiyarsu a cewar majiyoyi.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Mohammed Jalige, ya tabbatar da faruwar hatsarin tare da yi wa jami’an da suka rasu addu’a da kuma fatan samun sauki ga waɗanda suka jikkata.


Comments

One response to “Hatsarin mota ya ci rayukan ‘yan sanda uku a Kaduna”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Hatsarin mota ya ci rayukan ‘yan sanda uku a Kaduna […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *