Hatsarin mota a Yobe ya ci rayukan mutane 12

0
71
Hatsarin mota a Yobe ya ci rayukan mutane 12

Hatsarin mota a Yobe ya ci rayukan mutane 12

Daga Ibraheem El-Tafseer

Mutane 12 da suka haɗa da maza 10 da mata 2, sun rasa rayukansu a wani hatsarin mota a daren jiya Talata, 3 ga watan Disamba, 2024. Hatsarin ya auku ne a hanyar Bayamari zuwa Geidam a jihar Yobe.

Kwamandan hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC), reshen jihar Yobe, Livinus Yilzoom, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a birnin Damaturu.

A cewarsa, hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 10:00 na dare, kilomita 20, a ƙauyen Kyalluri, daura da hanyar Bayamari zuwa Geidam.

Ya bayyana cewa hatsarin ya haɗa da wata mota ƙirar HOWO dake tsaye mai lamba: MAG-831-ZR mallakin Kamfanin DAN NENE Construction da wata ƙaramar Bas Sharon mai lamba: BAU-124-YF wadda ta shiga ƙarƙashin babbar motar wadda nan take ta kama wuta.

Wanda hakan ne ya sabbaba ƙona mutane 12 da ke cikin motar bas ɗin da ko gane su ba a iya yi ba.

Mista Yilzoom ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa, tsayawar motar HOWO akan hanyar ne ya haifar da hatsarin, inda direban Sharon ke gudin wuce ƙa’ida, shi ne musabbabin hatsarin.

Ya kuma gargaɗi masu ababen hawa da su guji tafiye-tafiyen da dare saboda hatsarin rashin gani na ido, da kuma yanayin duhu, wanda yake ƙara ta’azzara da lallacewar yanayi a halin yanzu.

KU KUMA KARANTA: Hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutane 4

Ya kuma yi ƙira ga masu ababen hawa da su riƙa bin ƙa’idojin zirga-zirgar ababen hawa a kowane lokaci domin daƙile aukuwar lamarin nan gaba.

Kwamanda Yilzoom ya miƙa ta’aziyyar babban hafsan rundunar FRSC, Shehu Mohammed, ga iyalan wadanda suka rasu.

Leave a Reply