Harin ƙunar baƙin wake a Somaliya ya kashe sojoji 13

0
316

Wani ɗan ƙunar baƙin wake a Mogadishu babban birnin ƙasar Somaliya a ranar litinin ya kashe sojoji aƙalla 13 tare da raunata wasu aƙalla 20 a cikin wata makarantar soji a wani harin da ƙungiyar al Shabaab ta ɗauki alhakin kaiwa.

Gangamin soji da dakarun gwamnati da mayaƙan sa-kai suka ƙaddamar a shekarar 2022 ya tilastawa ƙungiyar da ke da alaƙa da al-Qaeda daga yankuna da dama a kudancin Somaliya, amma mayaƙan na ci gaba da kai munanan hare-hare.

A cikin ‘yan makonnin da suka gabata, yaƙin da sojoji ke kai musu ya tsaya cik a daidai lokacin da sojojin suka shirya kashi na biyu na farmaƙin, mayaƙan na al Shabaab sun zafafa kai hare-hare.

A ƙarshen watan Mayu, sun kashe aƙalla sojojin kiyaye zaman lafiya na Uganda 54 a wani sansani da ke kudancin Mogadishu.

KU KUMA KARANTA: Ɓarayi sun kai hari gidan yaɗa labarai, sun sace kayayyakin aiki a gidan rediyon Kogi

Kusan makwanni biyu sun yi ƙawanya a Baidoa, ɗaya daga cikin manyan biranen ƙasar.

Kuma sun kai jerin hare-hare a Mogadishu cikin wannan watan. Harin bam ɗin da aka kai ranar litinin ya auna makarantar sojoji ta Jale Siyaad.

Wani soja a asibitin sojoji na Mogadishu wanda ya bayyana sunansa a matsayin Ahmed ya ce yana da gawarwakin sojoji 13 da suka mutu da kuma wasu 20 da suka samu raunuka sakamakon fashewar.

Waɗanda abin ya shafa sun fito ne daga yankin Lower Shabelle kuma sun zo babban birnin ne don samun horo, in ji Captain Ali Farah, wanda ya san wasu daga cikinsu.

Ya ce yana sane da mutuwar mutane 10 zuwa yanzu. “An ƙirga sojojin ne a cikin jerin gwano lokacin da ɗan ƙunar baƙin wake ya tarwatsa kansa,” in ji Farah.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta Al Shabaab ta fitar ta ce maharin ya kashe sojoji 73 tare da jikkata wasu 124 na daban.

Ƙungiyar ta saba bayar da alƙaluman waɗanda suka mutu waɗanda suka fi na waɗanda hukumomi suka bayar.

Tun a shekara ta 2006 ne ƙungiyar Al Shabaab ke yaƙi domin hamɓarar da gwamnatin tsakiyar Somaliya tare da kafa nata mulkin bisa tsananin fassarar shari’ar Musulunci.

Leave a Reply