Harbi a wata makaranta a Amurka, ya hallaka mutane 4

0
75
Harbi a wata makaranta a Amurka, ya hallaka mutane 4

Harbi a wata makaranta a Amurka, ya hallaka mutane 4

Hukumomin tsaro sun bayyana cewa buɗe wutar da aka yi a wata babbar sakandire a jihar Georgia ta Amurka a ranar Laraba, ya hallaka aƙalla mutane 4 tare da raunata wasu 9.

Sai dai hukumomin sun sanar da kama ɗan bindigar da ake zargi.

Hukumar binciken manyan laifuffuka ta jihar Georgia ta bayyana cewar an kashe mutane 4, sai dai kai tsaye ba ta bayyana dalilin da ya sabbaba aikata hakan ba.

KU KUMA KARANTA:An yi musayar fursunoni tsakanin Amurka da Rasha

Saƙon da hukumar ta wallafa a shafinta na sada zumunta ya bayyana cewa, “an garzaya da ƙarin wasu mutanen 9 zuwa asibiti ɗauke da raunuka. Wanda ake zargi na tsare a hannun hukuma da ransa. Babu ƙamshin gaskiya a rahotannin da ke cewa an kashe shi.

Tun da fari, an samu rahoton cewa hukumomin makarantar sun aikewa iyayen dalibai da sakon cewar suna aiwatar da “wata tsatsaurar dokar hana zirga-zirga tun bayan samun rahoton bude wutar.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here