Hajji 2025: Saudiyya za ta hana masu matsananciyar jinya zuwa aikin Hajji

0
36
Hajji 2025: Saudiyya za ta hana masu matsananciyar jinya zuwa aikin Hajji

Hajji 2025: Saudiyya za ta hana masu matsananciyar jinya zuwa aikin Hajji

Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta fitar da sabbin sharuɗɗa na kiwon lafiya don tabbatar da tsaro da walwalar mahajjata, musamman ga maniyyata masu fama da wasu cututtuka.

Mutanen da ke fama da matsananciyar rashin lafiya ba za a ba su izinin gudanar da aikin Hajjin 2025 ba, kamar yadda mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Addini ta ƙasar, Muhammad Umar Butt ya bayyana.

Ya ce wannan matakin na da nasaba ne da yanayin tsananin zafi da rana da ake tsammanin za a yi a lokacin aikin Hajji, da kuma tabbatar da tsaro da kare lafiyar dukkan mahajjata.

KU KUMA KARANTA:NAHCON ta ƙaryata rahotanni kan ƙin fitar Alhazan Najeriya da dama daga Saudiyya

Kakakin ya ƙara da cewa ba za a bar masu fama da matsanancin ciwon ƙoda, zuciya, huhu, ciwon hanta da kuma ciwon daji ba su shiga aikin Hajji.

Bugu da ƙari, ya ce za a hana mutanen da suka kamu da cutar mantuwa , ko cututtuka masu yaɗuwa kamar su tarin fuka, tari, da sauran cututtuka makamantan haka yin aikin hajjin na baɗi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here