Habasha da Somaliland sun tattauna kan haɗin gwiwar soji

0
133

Manyan dakarun sojin Habasha da na Somaliland, yankin da ya ɓalle daga Somaliya sun yi wata ganawa a ranar Litinin a Addis Ababa, babban birnin ƙasar Habasha.

Kwamandojin sojin biyu sun tattauna batun haɗin gwiwar sojin ne a daidai lokacin da ake samun takun-saka tsakanin gwamnatin Somaliya da ke Mogadishu, da gwamnatin Habasha.

Hakan na zuwa ne bayan an ƙulla yarjejeniyar farko tsakanin ƙasar Habasha wadda ta ba da gabar ruwa, da Somaliland a farkon wannan watan kan buƙatar samun damar amfani da tashar jiragen ruwa ta tekun Bahar Maliya da ke Berbera a yankin na Somaliland.

KU KUMA KARANTA: Sojojin gwamnatin Habasha sun sake ƙwace ikon birnin Lalibela

A sanarwar da rundunar sojin Habasha ta fitar ta shafinta na Facebook a ranar Litinin, babban hafsan tsaro na rundunar sojojin ƙasar Habasha (ENDF) Field Marshal Birhanu Jula, da babban hafsan hafsoshin Soji na Somaliland Janar Nuh Ismail Tani, “sun tattauna kan hanyoyin da za a bi wajen aiki tare kan haɗin gwiwar soja.”

Ƙasar Somaliya ta yi watsi da yarjejeniyar tashar jiragen ruwa da Habasha ta ƙulla da Somaliland, tana mai ƙiran hakan da “haramtaccen” mataki, sannan kuma barazana ce ga hakkin makwabtaka da kuma cin zarafi kan ‘yancin-kan Somaliya.

Kazalika ƙasar ta yi wa jakadanta da ke Habasha ƙiranye bayan da aka sanar da yarjejeniyar.

Gwamnatin ƙasar Habasha ta kare matakin da ta ɗauka na sanya hannu kan yarjejeniyar ba tare da amincewar Mogadishu ba, tana mai cewa yarjejeniyarta da Somaliland ”ba za ta shafi wani ɓangare ko wata ƙasa ba.”

Yarjejeniyar ta bai wa Habasha damar samun wani sansanin sojin ruwa na dindindin, da kuma fannin hada-hadar ayyukan kasuwanci a mashigin tekun Aden.

Habasha ta yi asarar tashoshin jiragen ruwanta na Bahar Maliya a shekarun 1990 bayan yakin neman ‘yancin-kai na Eritriya, wanda ya gudana daga shekarar 1961 zuwa 1991.

A shekarar 1991 ne Eritriya ta samu ‘yancin-kai daga Habasha, wanda ya kai ga kafa ƙasashe biyu daban-daban.

Rabuwar ta sa Habasha ta rasa hanyar gabar ruwa ta isa Bahar Maliya kai-tsaye, da kuma manyan tashoshin jiragen ruwa.

Leave a Reply