Gwamnatin Yobe ta umarci a rufe dukkan makarantun kwana a faɗin jihar, saboda rashin tsaro
Gwamnatin Jihar Yobe ta ba da umarnin a rufe dukkan makarantun sakandare na kwana a faɗin jihar nan take a matsayin matakin kariya don tabbatar da tsaron ɗalibai.

A wata sanarwa da Mamman Mohammed, babban Darakta, Harkokin Yaɗa Labarai na Gwamnan Yobe ya fitar, ta ce umarnin ya zo ne bayan wani babban taron tsaro wanda Gwamna Hon. (Dr) Mai Mala Buni, CON, COMN, ya jagoranta tare da manyan shugabannin tsaro a jihar. Taron ya yi nazari kan abubuwan da suka faru kwanan nan na tsaro da suka shafi makarantu a sassan ƙasar, wanda hakan ya haifar da shawarar.
KU KUMA KARANTA: Rashin tsaro: Gwamnatin Najeriya ta rufe makarantun sakandire mallakin Gwamnatin tarayya
A cikin wata sanarwa da Dakta Bukar Aji Bukar, Sakataren dindindin na Ma’aikatar Ilimi ta Farko da Sakandare ya sanya wa hannu, gwamnati ta umarci a rufe dukkan makarantun kwana har sai yanayin tsaro ya inganta.
Gwamna Buni ya buƙaci ‘yan ƙasa da su kwantar da hankalinsu su ci gaba da addu’ar zaman lafiya, kwanciyar hankali, da kuma nasarar jami’an tsaro da ke aiki don kare rayuka da dukiyoyi a faɗin ƙasar.









