Gwamnatin Yobe ta ayyana gobe Talata a matsayin ranar hutu, don juyayin mutuwar Buhari
Gwamnan jihar Yobe Alhaji (Dr.) Mai Mala Buni CON COMN, ya amince da ayyana gobe Talata 15 ga Yuli, 2025, a matsayin ranar hutu don juyayin mutuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari GCFR wanda ya rasu ranar Lahadi a wani asibiti a Landan.
Gwamna Buni ya buƙaci ma’aikata da al’ummar jihar da su sadaukar da ranar domin yi wa marigayi shugaban ƙasa Muhammadu Buhari addu’ar samun gafara.
KU KUMA KARANTA: Gwamna Yobe ya ziyarci sansanin soji da ke Buni Gari, ya tallafawa iyalan Sojojin da aka kashe
Ya kuma umarci limamai da su yi amfani da wannan rana ta yadda za su yi addu’o’i a masallatan su ga marigayi shugaban ƙasa.
“Ya kasance shugaban da ya yi ƙoƙari wajen ganin an dawo da tsaro a jihar Yobe da ma yankin Arewa maso Gabas gaba ɗaya, ya cancanci wannan karramawa ta musamman daga al’ummar jihar,” Gwamna Buni ya ce.
A halin da ake ciki, majalisar zartaswar jihar a yau ta yi wani zama na musamman na addu’a ga marigayi shugaban ƙasa a madadin taronta na mako-mako wanda aka tsaya domin karrama marigayi tsohon shugaban ƙasar.
Tun da farko, Gwamna Buni, a cikin saƙon ta’aziyyar, ya bayyana marigayi Buhari a matsayin babban ɗan kishin ƙasa, wanda ya shafe tsawon rayuwarsa yana aikin tabbatar da haɗin kai da ci gaban Najeriya.
Ya ce Buhari mai tarbiyya ne, shugaba ne mai riƙon amana, kuma shugaba mai kishin ci gaban al’umma marar iyaka.
Gwamnan ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma sa Aljannah ce makomarsa.
KU KUMA KARANTA: Taron Gwamnonin Arewa Maso Gabas: Dole ne mu ƙarfafa haɗin kai don dakatar da matsalar tsaro – Gwamna Buni
Gwamna Buni ya jajantawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu GCFR, da iyalan marigayi tsohon shugaban ƙasa, gwamnatin jihar Katsina, Masarautar Daura da ma ‘yan Najeriya baki ɗaya bisa wannan babban rashi da aka yi.









