Gwamnatin Yobe ta amince da kuɗi Naira Biliyan 47 don ayyukan ci gaba a fannin noma, kiwon lafiya da samar da ayyukan yi

0
154
Gwamnatin Yobe ta amince da kuɗi Naira Biliyan 47 don ayyukan ci gaba a fannin noma, kiwon lafiya da samar da ayyukan yi
Gwamnan Yobe Dakta Mai Mala Buni

Gwamnatin Yobe ta amince da kuɗi Naira Biliyan 47 don ayyukan ci gaba a fannin noma, kiwon lafiya da samar da ayyukan yi

Majalisar Zartarwa ta Jihar Yobe ta amince da aiwatar da jerin manyan ayyukan ci gaba da suka kai kimanin naira biliyan 47, wani mataki ne da gwamnatin Hon. Dakta Mai Mala Buni ke ɗauka domin hanzarta ci gaban ababen more rayuwa, ƙarfafa samar da abinci, inganta kiwon lafiya da kuma samar da ayyukan yi a faɗin jihar.

An gudanar da taron majalisar ne a yau Laraba a gidan gwamnati da ke birnin Damaturu, ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar, Hon. Idi Barde Gubana wanda ya wakilci Gwamna Buni. A yayin zaman, an tantance kuma aka amince da dama daga cikin takardun bukatu da suka shafi sassa daban-daban na ci gaba.

Daga cikin muhimman abubuwan da aka amince da su har da naira biliyan 1.76 domin gina sabbin ofisoshi ga hukumomi guda biyar, ciki har da Hukumar Siyan Kayayyaki ta Jama’a (Bureau for Public Procurement), Hukumar Da’a da Tattalin Arziki (Fiscal Responsibility Board) da sauran su. Haka kuma, an amince da naira miliyan 962.6 don gina sabuwar hedikwatar Kamfanin Zuba Jari na Jihar Yobe (Yobe Investment Company Ltd).

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Yobe ya fi kowane Gwamna kula da harkar kiwon lafiya a jiharsa – Jaridar Blueprint

Haka zalika, majalisar ta amince da zuba jari a gine-ginen kasuwanci a jihar, ciki har da naira biliyan 2.78 domin gina Sabuwar Kasuwar Machina, naira biliyan 3.01 don karin kudin aikin Sabuwar Kasuwar Geidam, da kuma naira biliyan 3.98 domin kammala Sabuwar Kasuwar Potiskum. Baya ga haka, za a gina sabuwar tashar mota ta zamani a Damaturu da zai ci naira biliyan 6.13, sannan za a yi kwaskwarima ga tashar Yobe Line da kudin da ya kai naira miliyan 248.6.

A fannin noma, wanda ke daga cikin ginshikan ci gaban gwamnatin Buni, majalisar ta amince da naira biliyan 10.9 don sayen kayan aikin noma. Ciki har da naira biliyan 3.79 don kayan aikin noman damina, naira biliyan 1.38 da miliyan 480 don sayen famfunan ruwa masu amfani da hasken rana guda 1,902, da kuma naira biliyan 5.31 don taki irin na NPK.

Majalisar ta kuma amince da naira miliyan 396.9 don sake gina kofar ruwa da ta rushe a kauyen Alagarno da ke karamar hukumar Bade.

A bangaren kiwon lafiya, an amince da naira biliyan 1.43 don ayyukan gine-gine a asibitoci da cibiyoyin horaswa, da kuma naira biliyan 1.22 don sayen kayan aikin gwaje-gwaje da na lafiya ga asibitocin matakin biyu da na uku.

Domin inganta hanyoyin sufuri a jihar, majalisar ta amince da ayyukan gina hanyoyi da suka hada da: naira biliyan 1.24 don hanyar Daya zuwa Fadawa (5KM), naira biliyan 4.38 don hanyar Mashio zuwa Ngelzarma (18.5KM), naira miliyan 671.6 don hanyar Nahuta zuwa Ngojin (2.5KM), da kuma naira biliyan 5.36 don hanyar Damaturu zuwa Gambir.

KU KUMA KARANTA: Taron Gwamnonin Arewa Maso Gabas: Dole ne mu ƙarfafa haɗin kai don dakatar da matsalar tsaro – Gwamna Buni

A bangaren samar da ayyukan yi, musamman ga matasa, ma’aikatar kirkire-kirkire ta samu amincewar majalisa da naira miliyan 442.2 don bude sabbin shagunan gyaran gashi na zamani guda 100, da kuma naira miliyan 233.6 don bude shagunan gyaran gashin mata guda 50 a fadin jihar.

Don kara karfafa fannin lafiya, majalisar ta amince da daukar ma’aikatan lafiya 422, ciki har da ma’aikatan jinya da na lafiya da aka dauka a baya karkashin shirin MAMII (Maternal Mortality Reduction Innovation Initiative) a kananan hukumomi biyar na jihar.

Kwamishinan Harkokin Cikin Gida, Yada Labarai da Al’adu, Hon. Abdullahi Bego, wanda ya fitar da sanarwar ga manema labarai, ya jaddada kudirin Gwamna Buni na ci gaba da aiwatar da tsare-tsaren ci gaba da suka shafi kowa da kowa, yana mai nuni da kyaututtuka da yabo da gwamnatin ta samu a matakin kasa saboda ci gaba a fannin kiwon lafiya.

Majalisar ta jaddada cewa, wadannan amince-amincen suna daga cikin tsare-tsaren dabarun bunkasa rayuwar al’ummar jihar Yobe.

Leave a Reply