Gwamnatin soji ta Burkina Faso ta cire tambarin ƙungiyar ECOWAS a sabon fasfo da ta fitar

0
44
Gwamnatin soji ta Burkina Faso ta cire tambarin ƙungiyar ECOWAS a sabon fasfo da ta fitar

Gwamnatin soji ta Burkina Faso ta cire tambarin ƙungiyar ECOWAS a sabon fasfo da ta fitar

Ministan tsaron Burkina Fasfo, Mahamadou Sana ne ya ƙaddamar da sabon fasfo ɗin.

A tuna cewa Burkina Faso, Nijar da Mali, sun yanke hulɗa da ECOWAS, sakamakon takunkumin da aka ƙaƙaba musu saboda juyin mulkin da sojoji su ka yi.

Da ta ke mayar da martani, ECOWAS ta zargi ƙasashen uku da nufin tauye ‘yancin walwalar yankin

KU KUMA KARANTA:An ƙara wa sojojin Burkina Faso wa’adin shekaru biyar a kan mulki

Sana ya shaida wa manema labarai a wajen ƙaddamar da fasfo ɗin cewa sauyin ya zo ne ga matakin da Burkina Faso ta ɗauka na ficewa daga ƙungiyar ECOWAS, wadda aka yi a watan Janairu.

Ya ce, “A kan wannan fasfo, babu tambarin ECOWAS. Tun daga watan Janairu, Burkina Faso ta yanke shawarar janyewa daga wannan ECOWAS, kuma wannan shi ne kawai fahimtar matakin da Burkina Faso ta riga ta dauka.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here