Gwamnatin jihar Sakkwato ta ce ta fara biyan bashin shekaru uku na ɗaliban ta da ke karatu a Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato (UDUS).
Gwamnati ta sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna, (MoU), tare da Jami’ar don biyan kuɗin karatun ɗaliban jihar da aka karɓa a makarantar.
Sai dai gwamnatin jihar ta ka sa tura waɗannan kuɗaɗe tsawon shekaru uku, lamarin da ya sanya jami’ar ta UDUS ta hana ɗaliban da abin ya shafa shiga jarrabawa.
Nasiru Ɗantsoho, shugaban kwamitin tantancewar, ya bayyana a ranar Litinin cewa an kammala tantancewa kuma an fara tura kuɗaɗen da ba a biya ba.
KU KUMA KARANTA: Ɗangote ya ba da tallafin karatu ga al’ummar da ya gina kamfani a yankinsu
Ya ce wannan shiga tsakani ya biyo bayan rahotannin da ke cewa UDUS ta yi barazanar korar ɗaliban gida matuƙar ba a biya su gaba ɗaya ba.
Ɗantsoho ya ce kuɗaɗen waɗanda aka tantance za a biya su ne ga jami’ar domin baiwa ɗaliban damar rubuta jarabawar zango (semester) da kuma zaman karatu na gaba ba tare da wata matsala ba.
Shugaban kwamatin ya tunatar da cewa Gwamna Ahmad Aliyu, a lokacin da ya karɓi ragamar mulki ya nuna damuwarsa kan lamarin, wanda ya tilasta wa hukumar yin tunanin ƙin ɗaliban jihar.
Ya ce tsohuwar gwamnatin Aminu Tambuwal ta bar wa sabuwar gwamnati basussuka masu ɗimbim yawa, musamman a fannin bayar da tallafin karatu ga ɗalibai a ciki da wajen Najeriya.
“Halin da aka ƙi amincewa da ɗaliban mu ya sa mu fara tantancewa domin tabbatar da cewa Ɗaliban Sakkwato ne kaɗai ke cin gajiyar kuɗin.” inji shi
Shugaban ya ce kwamitin ya tantance dukkan ɗaliban da suka fito daga ƙananan hukumomin jihar 23 da ke karatu a UDUS.
Ya ƙara da cewa za a gudanar da irin wannan a wasu cibiyoyin idan buƙatar hakan ta taso.
Wasu daga cikin ɗaliban sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya cewa sun ji sauƙi, kuma sun nuna jin daɗinsu ga gwamnatin jihar kan wannan matakin.
Sun ƙara da cewa hakan ba ƙaramin ƙwarin gwiwa ba ne a gare su da a yanzu suka fuskanci karatunsu ba tare da wasa ba.