Gwamnatin tarayya ta ce ta shigar da naƙasassu 500, cikin tsarin inshorar lafiya na ƙasa, (NHIS), domin inganta hanyoyin samun ingantattun ayyukan kiwon lafiya.
Babban sakataren ma’aikatar jin ƙai da ci gaban jama’a, Dakta Sani Gwarzo, ne ya bayyana hakan a wani taron nuna alama na katin shaida na NHIS ga waɗanda suka amfana, ranar Laraba a Abuja.
A cewarsa, matakin zai tabbatar da samar da lafiya mai araha ga naƙasassu a faɗin ƙasar.
KU KUMA KARANTA: An haifi jariri na farko ta hanyar IVF a Asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya
Gwarzo ya bayyana haka ne a lokacin da ya jagoranci tawagarsa zuwa fadar sarkin gargajiya kuma shugaban naƙasassu da ke Karo Majiji a Abuja.
Hukumar kula da naƙasassu ta ƙasa NCPWD ce ta ɗauki nauyin yin rajistar. An yi atisayen ne domin rage wahalhalun da naƙasassu ke fuskanta wajen samun aiyukan kula da lafiya mai sauƙi.
Ya ce gwamnati ta fara aiwatar da shirin na gwaji a babban birnin tarayya kuma ana sa ran za a kai har zuwa jihohi 36 na tarayya.
Har ila yau, Sakataren Zartaswa, NCPWD, James Lalu, ya tabbatar wa naƙasassu ƙudirinsa na tallafa wa jin daɗinsu da ilimin ’ya’yansu, don tabbatar da kyakkyawar makoma a cikin al’ummar naƙasassu.
Hukumar, in ji shi, ta samar da guraben aikin yi ga naƙasassu a ma’aikatun gwamnati, sassan da hukumomi, MDAs.
“Wannan shi ne cikar kashi biyar na guraben aikin yi ga naƙasassu bisa ga dokar kafa NCPWD,” in ji shi.
Ya kuma yabawa tsohon kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila bisa yadda yake ƙara yawan kaso na guraben aikin yi ga naƙasassu a ƙasar nan.
Mista Lalu ya jaddada ƙudirinsa na ganin an samar da wurin da aka ware na dindindin da nufin gina gidajen naƙasassu a yankin Zuba na babban birnin tarayya Abuja.
Da yake mayar da martani, Mohammed Ɗantani, wanda ya yi magana a madadin fadar, ya buƙaci gwamnati ta tallafa wa ilimin ‘ya’yansu.
Mista Ɗantani, wanda kuma shi ne Sakataren ƙungiyar naƙasassu ta FCT, ya gode wa gwamnatin tarayya bisa goyon bayan da take bayarwa wajen inganta rayuwar naƙasassu a babban birnin tarayya Abuja.
Sai dai ya yi ƙira da a tura ƙarin malamai zuwa makarantar firamare da ke yankin, inda ya ƙara da cewa ana ta fama da matsalar ƙarancin ma’aikata.
“Malamai uku ne kawai ga ɗalibai sama da 200 a makarantar. “Muna ƙira ga gwamnati da ta ƙara yawan adadin malamai domin taimaka wa yaran mu su samu ingantaccen ilimi.
“Ba ma son yaranmu su kasance a kan titi suna bara kamar yadda muke yi. Don Allah a taimaka a tabbatar da makomar yaranmu da ingantaccen ilimi,” inji shi.