Gwamnatin Najeriya ta rufe kwalejojin ilimi 22, waɗanda aka buɗe su ba bisa ƙa’ida ba

0
300
Gwamnatin Najeriya ta rufe kwalejojin ilimi 22, waɗanda aka buɗe su ba bisa ƙa'ida ba

Gwamnatin Najeriya ta rufe kwalejojin ilimi 22, waɗanda aka buɗe su ba bisa ƙa’ida ba

Hukumar Kula da Kwalejojin Koyar da Malamai a Nijeriya (NCCE), ta sanar da rufe kwalejoji 22 da ke aiki ba bisa ƙa’ida ba a sassa daban-daban na ƙasar.

Hakan ya zo ne a wani samame da hukumar ta gudanar kan makarantun bogi da ake amfani da su wajen cutar da al’umma.

Nasarorin da hukumar ta gabatar ya tabbatar da wannan mataki, wanda aka ce ya zama wajibi don kare martabar ilimi a Najeriya.

Hukumar ta ce baya ga rufe kwalejojin bogi, ta gudanar da bincike kan ma’aikata da kuma sa ido kan harkokin kudi a dukkan manyan kwalejojin koyar da malamai 21 na tarayya a Nijeriya.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin tarayya ta amince da Kwalejojin ilimi su fara ba da shaidar takardar karatun Digiri na ƙashin kansu

Matakin ya nuna cewa hukumar ba wai kawai ta tsaya ne kan gano makarantun bogi ba, har ma tana tabbatar da bin ka’idojin aiki a makarantun gwamnati.

A baya-bayan nan shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga hukumomin ilimi da su tsananta yaki da makarantun bogi da ke bata tsarin ilimi.

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban ya bayyana haka ne a yayin bikin kammala karatu karo na 14 na jami’ar NOUN da aka gudanar a Abuja.

Shugaban, wanda wakiliyarsa, Rakiya Ilyasu ta isar da sakon nasa, ya ce ba za a lamunci lalata nagartar tsarin ilimi ba domin gudun ruguza makomar ɗaliban Nijeriya.

Tinubu ya jaddada cewa gwamnati tana da kudurin karfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin da ke kula da ilimi domin inganta harkokin karatu.

KU KUMA KARANTA: Ma’aikatar ilimi ta tarayya, ta yaba da ci gaban da Gwamnatin Yobe ta samu a fannin Ilimi

Ya ce hukumomin JAMB, NYSC, NUC, NBTE da NCCE suna aiki tare wajen ganin an kawar da batun takardun bogi da kuma makarantu marasa sahihanci a Nijeriya.

Rufe kwalejojin bogi 22 da NCCE ta yi ya nuna kokarin gwamnati na kare martabar makarantu na Nijeriya.

Ana ganin idan aka ci gaba da irin haka, za a iya rage yawaitar makarantun bogi da kuma tabbatar da cewa duk wanda ya kammala karatu a Nijeriya ya cancanci shaidar da ya samu.

Leave a Reply