Gwamnatin Najeriya ta amince da kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu guda 9 a faɗin ƙasar

0
260
Gwamnatin Najeriya ta amince da kafa sabbin jami'o'i masu zaman kansu guda 9 a faɗin ƙasar
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu

Gwamnatin Najeriya ta amince da kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu guda 9 a faɗin ƙasar

Daga Jameel Lawan Yakasai

Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya sanar da hakan ranar Laraba, yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasa, bayan taron majalisar zartarswa ta ƙasa da shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a Abuja.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin tarayya ta dakatar da samar da sabbin jami’o’i a ƙasar 

Ya ce jami’o’in da aka amince da su sun haɗa da:

Jami’ar Tazkiyah da ke jihar Kaduna
Jami’ar Leadership da ke babban birinin tarayya, Abuja
Jami’ar Jimoh Babalola a jihar Kwara
Jami’ar Bridget, Mbaise a jihar Imo
Jami’ar Greenland da ke jihar Jigawa
Jami’ar JEFAP a jihar Neja
Jami’ar Azione Verde da ke jihar Imo
Jami’ar Unique Open a Jihar Legas
Jami’ar American Open da ke Jihar Ogun

Leave a Reply