Gwamnatin Kano ta samar da inshorar lafiya ga fursunoni
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da shigar da fursunonin cikin tsarin kiwon lafiyar, domin basu damar cin gajiyar ingantaccen tsarin kiwon lafiya kyauta yayin da su ke tsare.
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ta shigar da ɗaurarru cikin tsarinta na ɗaukar nauyin kiwon lafiya da nufin samar musu da ingantaccen tsarin kiwon lafiya kyauta yayin da suke ɗaure.
Hakan na ƙunshe ne a cikin sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kula da gidajen gyaran hali na Kano, csc Musbahu Kofar-Nasarawa ya fitar, a jiya Litinin a Kano.
Kofar-Nasarawa ya ruwaito babbar sakatariya a hukumar kula da kiwon lafiya ta jihar Kano, Dr. Rahila Aliyu-Mukhtar, na bayyana hakan yayin ziyarar data kaiwa shugaban hukumar kula da gidajen gyaran hali na Kano, Controller Ado Salisu, a ofishinsa.
KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Gombe ta yi wa Almajirai 1,000 rajistar inshorar lafiya
Rahila Aliyu-Mukhtar tace Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da shigar da daurarrun cikin tsarin kiwon lafiyar, domin basu damar cin gajiyar ingantaccen tsarin kiwon lafiya kyauta yayin da su ke tsare.
“Walwalar fursunoni ta ɓangaren kiwon lafiya nada mahimmancin gaske a ɓangaren gudanar da gidajen yari yadda ya dace da kuma samun nasarar gyaran halayya da sake tsugunar dasu da sake mayar dasu cikin al’umma,” a cewarta.









