Gwamnatin Kano ta Haramta Bikin “Ƙauyawa day” a faɗin Jihar

0
169
Gwamnatin Kano ta Haramta Bikin "Ƙauyawa day" a faɗin Jihar

Gwamnatin Kano ta Haramta Bikin “Ƙauyawa day” a faɗin Jihar

Daga Shafaatu Dauda Kano

Hukumar tace fina-finai a jihar Kano ta sanar da haramta bukukuwan “Kauyawa Day” da ake yi a faɗin jihar, a wani mataki na ƙarfafa kyawawan ɗabi’u tsakanin al’umma da kuma bin doka.

Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha ne ya sanar da matakin yayin wani taron manema labarai a yau Asabar 17 ga Mayun 2025, inda ya ce an kuma dakatar da dukkan wuraren event centres daga gudanar da bukukuwan.

KU KUMA KARANTA:Hukumar Hizba a Kano, ta haramta sauraron waƙar ‘Amanata’ ta Hamisu Breaker

El-Mustapha ya ce wannan mataki da suka ɗauka wani ɓangare ne da hukumar ke yi na ƙarfafa ɗabi’u masu kyau tsakanin al’umma.

“Wannan mataki da muka ɗauka yana cikin tsarin dokar hukumar mu wanda majalisar jiha ta yi garambawul da kuma gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya wa hannu,” in ji El-Mustapha.

Ya ƙara da cewa dokokin sun bai wa hukumar tace finai-finai ta jihar Kano damar kula da kuma sa ido kan ayyukan DJ (waɗanda ke saka waƙoƙi a bukukuwa) ke yi da kuma dukkan wuraren bukukuwa a faɗin jihar Kano.

Ya kuma yi kira ga shugabannin al’umma da jami’an tsaro, ciki har da Hisbah da ƴan bijilanti da su haɗa-kai da hukumar su domin tabbatar da cewa an bi wannan mataki na haramta bukukuwan ƙauyawa sau da kafa

Leave a Reply