Gwamnatin Kano ta hana sayar da ruwan jarkoki a faɗin jihar
Daga Shafaatu Dauda Kano
Gwamnatin jihar Kano ta sanar da hana amfani da ruwan jarkoki ko kuma sayarwa ga jama’a ruwan har sai an tabbatar da ingancinsa a dakin gwaje gwaje.
Kwamishinan muhalli da sauyin yanayi na jihar Kano,Dr Dahir Muhammad Hashim ya bayyana hakan a lokacin bude hukumar dake kula da dakunan gwaje gwajen abubuwan dake haddasa sauyin yanayi wacce aka sake yiwa garambawul a birnin Kano.
Kwamishinan yace an sake yiwa hukumar yaki da gurbacewar muhalli ta jihar Kano garambawul ne saboda yanayin da ake ciki na yawan samun sauye sauyen yanayi a wure masu zafi ciki harda Kano.
Ya nemi ma’aikatan hukumar da su bada hadin kan da ya dace domin samar da kyakkyawan muhalli a jihar Kano.
A yayinda yake karin haske,mai bada shawara kan harkokin sauyin yanayi da tsaftar muhalli ga kwamishinan muhalli na jihar Kano,Farfesa Aliyu Baba Nabegu wanda ya halarci taron kuma daya daga cikin masu kula da dakunan gwaje gwajen sauyin yanayi,yace gwamnatin Kano zata fara gwada ruwan da ake sayarwa a jarkoki ga jama’a a dakin gwaji kafin sayarwa da jama’a.
KU KUMA KARANTA:Matsalar ruwan sha, Gwamnatin Kano za ta kai ɗauki a Warawa – Kwamishinan Muhalli
Yace mahimmacin hakan yana daga cikin tabbatar da tsaftar muhalli da abinda kar cikin muhallin.
Neptune prime Hausa ta rawaito cewa, gwamnatin Kano zata hada harda ruwan leda da ake sayarwa a Kano.
“Ba zamu bari jama’a su rika shan gurbataccen ruwa a Kano ba ,zamu rika zuwa har Inda yan garuwa ke debo ruwa ana kaiwa dakin gwaji domin tabbatar da ingancinsa kafin sayarwa da jama’a,”Inji Farfesa Nabegu.
Daga nan ya nemi jama’a su rika kula da irin iskar da suke shaka ,dan gujewa samun kai a yanayi mara kyau.
Yace har masu sayar da kifi za’a rika bibiyarsu domin tabbatar dacewa basa sayar da kifi mara kyau bayan gwadawa a dakin gwaje gwaje.