Gwamnan Zamfara ya ƙaddamar da motocin bas 50 don sauƙaƙa zirga-zirga a al’ummar jihar 

0
251
Gwamnan Zamfara ya ƙaddamar da motocin bas 50 don sauƙaƙa zirga-zirga a al'ummar jihar 
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal Dare

Gwamnan Zamfara ya ƙaddamar da motocin bas 50 don sauƙaƙa zirga-zirga a al’ummar jihar

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da sabbin motocin masu cin mutum kujera 18 gida 50 ga Kamfanin sufuri na Jihar Zamfara (ZTC).

Yayin ƙaddamar da motocin a ranar Alhamis, Gwamnan ya ce wannan matakin cika alkawari ne da gwamnatinsa ta dauka, tare da barin tarihi mai kyau ga jihar.

A cewar wata sanarwa daga mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Idris, sabbin motocin da aka saya na zamani ne, masu ɗauke da na’urar bada sanyi (AC), kuma an ƙera su ne da la’akari da jin daɗi da tsaron fasinjoji.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Zamfara ya jagoranci taron majalisar zartaswar jihar, ya karɓi rahoton kwamitin ‘yan fansho

Yayin da yake jawabi a wajen bikin ƙaddamarwar, Gwamna Lawal ya ce wannan shiri sabuwar kafa ce da aka dasa a tafiyar da mulki a Zamfara, wadda ta mayar da hankali kan gaskiya da rikon amana da kawo cigaba mai dorewa.

“Wasu da dama suna tambaya dalilin jinkiri tsakanin isowar motocin da fara amfani da su. A da, wasu gwamnatoci da zaran motoci sun iso sai su ƙaddamar da su cikin gaggawa dan kawai ace suna aiki. Amma mu gwamnatin mu ta daban ce—ba mu yarda da gaggawa inda kula da hankali ya fi muhimmanci ba,” in ji shi.

Gwamnan ya bayyana cewa jinkirin da aka samu da manufa aka yi shi ne, domin ba da dama ga gwamnati ta gina tsarin da zai tabbatar da gaskiya, kulawa, da kyakkyawan shugabanci wajen amfani da motocin.

Leave a Reply