Gwamnan Yobe ya halarci jana’izar Sarkin Gudi a garin Gadaka
Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Dakta Mai Mala Buni CON, a yau juma’a, ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar wajen jana’izar marigayi Sarkin Gudi, Alhaji Isah Bunuwa Madubu Ibn Khaji, wanda ya rasu jiya a asibitin Nizameye dake Abuja bayan ya sha fama da jinya.
Gwamna Buni da ke halartar wani taro a Abuja ya katse ayyukansa domin halartar jana’izar marigayi Sarkin da kansa.
KU KUMA KARANTA: Sarkin Dutse Mai martaba Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi ya rasu a Abuja

Gwamna Buni ya samu rakiyar kakakin majalisar dokokin jihar Yobe Hon. Chiroma Buba Mashio, Sanata Mohammed Ibrahim Bomoi, Sanata Musa Mustapha, da ‘yan majalisar wakilai.
Sauran sun haɗa da sakataren gwamnatin jihar Baba Malam Wali, ‘yan majalisar dokokin jihar, Hon. kwamishinoni, masu ba da shawara na musamman, shugabannin kananan hukumomi, Sarakuna, Malamai, jiga-jigan jam’iyya da dubban magoya bayansa.
Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya gafarta masa kurakuransa.

Ya kuma yi kira ga al’umma da su tsaya tsayin daka, kuma su yafe wa juna, domin “kowa zai mutu, a yaushe ne, a ina da kuma yadda Allah Ta’ala ya sani.
Gwamna Buni ya bayyana rasuwar mai mary sarkin a matsayin babban rashi ga dangi, masarautar Gudi, jihar Yobe da kuma Najeriya.









