Gwamnatin Kano, ta ware naira biliyan 8 don gina manyan makarantun firamare guda uku a faɗin jihar.
Gwamna Abba Yusuf ya ce makarantun, za su kasance da cikakkun wuraren karatu, wanda hakan zai ba da isasshen yanayi ga yaran da suka fito daga iyaye matalauta don samun ingantaccen ilimi domin samun ci gaba a nan gaba.
Gwamnan ya ce za a samar da waɗannan makarantun ne a kowace mazaɓar majalisar dattawa da kayayyakin koyo na zamani don samar da ilimi mai inganci a matakin farko.
Ya kuma ce an ware naira biliyan 6 domin gyara dukkan makarantun firamare.
Hakazalika, ya ce gwamnati ta amince da gyara wasu cibiyoyi na musamman guda 26 da tsohon Gwamna Rabi’u Kwankwaso ya ƙirƙiro kuma an kammala 17.
KU KUMA KARANTA: Najeriya na buƙatar ƙarin makarantu 20,000, ajujuwa 907,769 – UBEC
“Za mu ci gaba da ba da kulawa ga samar da kayan aikin koyarwa na yau da kullum zai ba wa yaranmu damar samun ingantaccen yanayin koyo da koyarwa.
“Mun kuma kashe naira miliyan 500 wajen gina dakin kwanan ɗalibai a Jami’ar Aliko Ɗangote dake Wudil sannan kuma an biya naira miliyan 150 don sabon sashin kula da muhalli da yanayi na Jami’ar Maitama Sule.
“An biya naira Miliyan 500 na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jiha don sabbin kwasa-kwasai a Wudil da Jami’ar Yusuf Maitama Sule.
“Masu karatun shari’a na Kano da sauran cibiyoyi sun ci gajiyar biyan sama da naira miliyan 100 domin yin rijistar sabbin kwasa-kwasansu.
“Kimanin kashi 93 cikin 100 na kuɗaɗen karatu na ɗaliban Masters 501 a Indiya da sauran ƙasashen waje an daidaita su kuma an daidaita alawus ɗin su na tsawon watanni huɗu don ba su damar fuskantar karatunsu,” in ji shi.
Gwamna Abba ya kuma ce gwamnati ta biya naira miliyan 700 a matsayin kuɗin rijista ga ɗaliban jihar Kano da ke karatu a jami’ar Bayero ta Kano, sannan ta biya naira biliyan 1.5 a matsayin kuɗin jarrabawar WAEC da NECO ga ɗaliban makarantun sakandire na jihar.