Gwamnan Kano ya ba da tallafin Naira Miliyan 100 ga waɗanda gobara ta shafa a kasuwar Kantin Kwari.

0
59
Gwamnan Kano ya ba da tallafin Naira Miliyan 100 ga waɗanda gobara ta shafa a kasuwar Kantin Kwari.

Gwamnan Kano ya ba da tallafin Naira Miliyan 100 ga waɗanda gobara ta shafa a kasuwar Kantin Kwari.

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanar da bayar da tallafin Naira Miliyan Dari ga wadanda gobara ta kone musu shaguna a shahararriyar kasuwar Kantin Kwari, a madadin gwamnatin jihar Kano.

Gwamnan ya bayyana tallafin ne yayin da ya jagoranci wasu manyan jami’an gwamnati ziyarar ta’aziyya zuwa kasuwar a yau.

A Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ta nakalto Gwamna Abba Kabir Yusuf yana mika jaje ga yan kasuwar da gobarar ta shafa.

Gwamnan ya ce tallafin ba diyya ba ne ga asarar da aka yi, sai dai don rage radadin barnar da aka yi wa yan kasuwar da abin ya shafa.

Alhaji Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da shirin gwamnatin Kano na inganta yanayin kasuwanci a kasuwar ta hanyar girka fitilun hasken rana, gyaran hanyoyi, gina magudanun ruwa da kuma samar da rijiyoyin burtsatse da sauran su.

KU KUMA KARANTA:Atiku ya tallafawa ‘yan kasuwar Kantin kwari da Naira miliyan Hamsin

Ya yi kira ga shugabannin kasuwar da su fara shirye-shiryen da za su taimaka wa dimbin yan kasuwar wajen gudanar da harkokinsu cikin sauki, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta yi duk mai yiwuwa don Kano ta ci gaba da zama cibiyar kasuwanci a Arewacin Najeriya da wasu kasashen Yammacin Afirka.

Tun da farko, Manajan Darakta na Hukumar Gudanar da Kasuwar Kantin Kwari, Alhaji Hamisu Sa’ad Dogon Nama, ya bayyana cewa shaguna 29 ne gobarar ta kone, kuma ya gode wa jami’an hukumar kashe gobara da wasu da suka taimaka wajen dakile yaduwar gobarar.

Shugaban kwamitin dattawan kasuwar, Alhaji Sabi’u Bako, ya gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan kulawarsa ga halin da yan kasuwar da abin ya shafa ke ciki, tare da rokon goyon bayan gwamnan wajen magance wasu daga cikin matsalolin da ke hana kasuwar gudanar da aiki cikin sauki.

Leave a Reply