No menu items!

Sample Page Title

Date:

Gwamnan Jihar Bauchi, Alhaji Bala Abdulƙadir Muhammad ya zama shugaban ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP na ƙasa baki ɗaya.

Bala wanda ya samu nasarar ɗare wa kujerar ne a wani taron da zaɓaɓɓun gwamnonin suka gudanar a Jihar Bauchi da ya samu halartar Gwamnonin tare da Atiku Abubakar.

Da yake sanar da sakamakon zaɓen nasu, gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya ce, sun cimma matsayar ne bisa lura da cewa Bala Muhammad zai iya jagorantar ƙungiyar yadda ya kamata.

KU KUMA KARANTA: Sake zaɓen Fintiri, nasara ce ga demokraɗiyya – PDP

Kazalika, ya sanar da cewa gwamnonin PDP ɗin sun kuma zaɓi gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara a matsayin mataimakin shugaban ƙungiyar.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...