Gwamna Zulum ya ba da umarnin a binciki likitocin da suka ƙi karɓar mutanen da suka yi hatsarin mota

1
892

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya jagoranci binciken ma’aikatan asibitin Maiduguri da ake zargin sun ƙi amincewa da waɗanda hatsarin ya rutsa da su.

Gwamnan ya umurci ma’aikatar lafiya ta yi bincike tare da kamo ma’aikatan lafiya da ke bakin aiki bisa zargin ƙin amincewa da waɗanda hatsarin ya rutsa da su asibitin Umaru Shehu UltraModern Hospital da ke birnin Maiduguri.

Zulum ya ba da umarnin ne a ranar Alhamis a sashin bada agajin gaggawa na asibitin.

KU KUMA KARANTA: An rantsar da Zulum, ya godewa al’ummar jihar Borno da suka sake zaɓensa a karo na biyu

Ziyarar da gwamnan ya kai cibiyar martani ne ga wani faifayin bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta wanda ke nuna yadda wasu jami’an kiwon lafiya suka ƙi amincewa da waɗanda haɗarin ya rutsa da su da aka kawo asibiti.

Ya ba da sa’o’i 24 ga ƙungiyar bincike don gano ma’aikatan kiwon lafiya da abin ya shafa da kuma ba da shawarar takunkumin da suka dace.

“Abin da ya faru bai dace ba kuma ba za a amince da shi ba,” in ji gwamna Zulum yayin da yake jawabi ga ma’aikatan lafiya a asibitin.

“Yanayin da aka bar marasa lafiya suna kuka don neman taimako, amma asibiti ya ƙi su? Ba za mu ƙyale irin wannan yanayin ya maimaita kansa ba.

“Ban ga dalilin da zai sa ba za a ɗauki matakin ladabtarwa a kan ma’aikatan da suka yi kuskure a wannan asibitin ba.

Zulum ya ce “Idan duk wani likita ko wani ma’aikaci a kowane ɗayan wurarenmu ba ya son zuwa wurin marasa lafiya ba tare da wani dalili ba, to ya kamata a kore shi ko ita ba tare da jinkiri ba,” in ji Zulum.

Ya ba da umarnin cewa: “A cikin sa’o’i 24 masu zuwa, ya kamata Hukumar Kula da Asibitoci da Ma’aikatar Lafiya su binciki lamarin tare da tabbatar da ɗaukar matakan ladabtarwa ga duk waɗanda ke bakin aiki da suka ƙi karɓar waɗanda haɗarin ya rutsa da su.”

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta zuba maƙudan kuɗaɗe a fannin kiwon lafiya, gami da jin daɗin jami’an kiwon lafiya a faɗin jihar.

Don haka ya yi ƙira ga jami’an kiwon lafiya da su mayar da hankali wajen samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga duk majinyata ba tare da nuna bambanci ba.

1 COMMENT

Leave a Reply