Gwamna Raɗɗa ya yi alƙawarin tallafin karatu ga ‘yan asalin Katsina da su ka haddace Alƙur’ani

0
271
Gwamna Raɗɗa ya yi alƙawarin tallafin karatu ga 'yan asalin Katsina da su ka haddace Alƙur'ani
Gwamnan Katsina, Dakta Umar Raɗɗa

Gwamna Raɗɗa ya yi alƙawarin tallafin karatu ga ‘yan asalin Katsina da su ka haddace Alƙur’ani

Gwamna Dikko Radda na Jihar Katsina ya yi alkawarin bayar da tallafin karatu na musamman ga ‘yan asalin jihar da suka haddace Alƙur’ani Mai Tsarki kuma suna da a ƙalla kiredit biyar a darussan da ake bukatar a yi digiri a fannin ilimin likitanci da na kiwon lafiya.

Radda ya bayyana hakan ne a wani taron yini guda da aka shirya tare da masu ruwa da tsaki, wanda Hukumar Kididdiga ta Jihar Katsina ta shirya a jiya Litinin, domin tattaunawa kan gyara tsarin karatun tsangaya da na Islamiyya.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Katsina ya saka hannu kan dokar haramta ɓoye abinci

A cewarsa, duk wani ɗan asalin jihar da ya haddace Alƙur’ani kuma ya cika sharuddan da ake buƙata, zai iya miƙa shaida, domin gwamnatin jihar za ta ɗauki nauyin karatunsa tun daga farko har zuwa ƙarshe.

Gwamnan ya ƙara da bayyana cewa, ta hannun Hukumar Ilimin Addinin Musulunci, gwamnatin jihar za ta fara shirya gasa ga marubutan Alƙur’ani a Jihar Katsina.

Leave a Reply