Gwamna Buni ya bada tallafin naira miliyan 100 ga waɗanda gobarar kasuwar Damaturu ta shafa

0
152

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Gwamnan  jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya bayar da gudunmuwar N100m ga waɗanda gobara a kasuwar waya ta Damaturu ta shafa.

A wata sanarwa dake ɗauke da sa hannun babban daraktan yaɗa labarai na gwamna Buni, Mamman Mohammed ya ce gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci wurin da gobarar ta tashi domin jajanta wa waɗanda abin ya shafa.

Gwamna Buni ya bayyana afkuwar gobarar a matsayin abin takaici da kuma babbar asara ga ɗaiɗaikun mutanen da lamarin ya shafa da kuma jihar baki ɗaya.

“Abin takaici ne yadda wannan bala’i ke faruwa a yanzu yayin da matasanmu ke ƙoƙarin gina sana’o’insu.”

“Gwamnati za ta ci gaba da taimaka muku wajen dawowa kan sana’o’in ku, domin samar da ƙarin ayyukan yi ga matasan mu.”  in ji Buni.

KU KUMA KARANTA: Tashin gobara a kasuwar waya a Damaturu, an yi asarar dukiya mai yawa

Gwamnan ya kuma umurci sakataren gwamnatin jihar da ya raba shaguna ga waɗanda abin ya shafa a sabuwar kasuwar zamani ta Ibrahim Gaidam da aka gina a Damaturu.

Ya kuma ƙara umartar ma’aikatar gidaje ta jihar da ta tantance irin ɓarnar da aka yi da nufin sake gina shagunan da abin ya shafa ga masu su.

Buni ya  kuma yi ƙira ga jama’a da su yi taka tsantsan tare da ɗaukar matakan da suka dace kan abubuwan da za su iya haifar da bala’in gobara a gida da wuraren kasuwancin su.

Leave a Reply