Gwamna Abba ya kafa kwamitin binciken sayar da mayanka ta Chalawa da Gwamnatin Ganduje ta yi

0
131
Gwamna Abba ya kafa kwamitin binciken sayar da mayanka ta Chalawa da Gwamnatin Ganduje ta yi

Gwamna Abba ya kafa kwamitin binciken sayar da mayanka ta Chalawa da Gwamnatin Ganduje ta yi

Daga Jameel Lawan Yakasai

Sakataren Gwamnatin Kano, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya ƙaddamar da kwamitin mutane 11 da zai binciki batun sayar da Mayanka ta Najeriya (NIMAP Abattoir) da ke Chalawa Industrial Area, wanda gwamnatin da ta gabata ta Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta yi.

Tun farko, Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayyana wannan mu’amala a matsayin “mummunan aiki” da ya janyo rugujewar wannan katafariyar Mayanka, wacce ita ce ta farko irinta a Najeriya.

KU KUMA KARANTA: Kwankwaso da Ganduje ku haƙura da rikicin siyasar nan haka domin ci gaban Kano – Kashim Shettima

A wajen kaddamar da kwamitin ranar Laraba, Sakataren Gwamnati ya bayyana cewa aikin kwamitin ya haɗa da:

– Binciken yanayin yadda aka sayar da filin da kayan aikin.

– Nazarin takardu da yarjejeniyoyin da suka shafi cinikin.

– Tantance ko an bi dokoki da ka’idojin gwamnati.

– Gano mutanen da suke da hannu a sayarwar tare da bada shawarar hukunci.

– Dawo da kadarori ko kudaden gwamnati da aka rasa.

– Bayar da shawara kan yadda za a kafa sabuwar Mayanka ta zamani mai bin ka’idojin ƙasa da ƙasa.

Kwamitin zai gabatar da rahotonsa cikin makonni uku.

Tsohon shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci ta Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, ne shugaban kwamitin tare da Abdulkadir Shehu daga ofishin Ma’aikatar Albarkatun Ƙasa a matsayin sakatare.

A cikin sauran mambobi akwai:

– Kwamishinan Harkokin Jin Kai, Alhaji Adamu Aliyu Kibiya,

– Magajin Garin Kano, Alhaji Nasiru Inuwa Wada,

– Mashawarcin Gwamna kan Harkokin Doka, Barista Aminu Hussain,

– Muhammad Yusuf Danduwa,

– Barista Hamza Nuhu Dantani,

– Alhaji Muhammad Aminu Inuwa,

– Barista Amina Umar Garba,

– Barista Bashir Sabiu, da

– Muhammad Yusuf (Co-Secretary).

Leave a Reply