No menu items!

Sample Page Title

Date:

Daga Ibraheem El-Tafser

Hukumomi a Sifaniya sun ce aƙalla mutane 11 ne suka mutu sakamakon gobara da ta tashi a wani gidan rawa a birnin Murcia da ke kudu maso gabashin ƙasar.

Gobarar ta tashi ne a wani shahararren gidan rawa a yankin Atalayas, da safiyar ranar Lahadi.

Wani bidiyo da ya karaɗe intanet ya nuna yadda wuta ke ci a ginin da kuma hayaƙi da ya turnuƙe sama.

Ma’aikatan bayar da agajin gaggawa na can suna neman mutanen da suka ɓata kuma ke cikin harabar gidan rawan lokacin da wutar ta tashi.

Magajin garin Murcia Jose Ballesta ya faɗa wa tashar talabijin ta Spain 24, cewa an ayyana zaman makoki na kwanaki uku a garin.

Mutane sun fara isa gidan rawan domin ƙoƙarin neman ‘yan’uwansu da suka ɓata.

Jami’an agajin sun ce sun gano gawawwaki shida zuwa yanzu.

Kawo yanzu dai ba a kai ga gano abin da ya haddasa gobarar ba, wadda ta tashi a lokacin da gidan rawan ke cike da mutane.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...