Gidauniyar Atiku ta ba da tallafin karatu ga ‘yan mata 3 da su ka yi nasara a gasar Ingilishi ta duniya

0
190

Gidauniyar Atiku ta ba da tallafin karatu ga ‘yan mata 3 da su ka yi nasara a gasar Ingilishi ta duniya

Daga Jameel Lawan Yakasai

Gidauniyar Atiku Abubakar ta bayar da tallafin karatu ga ɗalibai uku ‘yan Najeriya da su ka lashe manyan lambobin yabo a gasar TeenEagle Global Round ta 2025 da aka gudanar a birnin London, ƙasar Birtaniya.

Nafisa Aminu, Rukayya Fema, da Hadiza Kalli ne suka wakilci tawagar Najeriya a wannan gasa ta duniya a bana.

KU KUMA KARANTA: Shugaba Tinubu ya taya gwaraza ‘yan jihar Yobe da suka lashe gasar turanci a Landan murna

Nafisa Aminu mai shekaru 17 ce ta zama ta fi kowa fice a fannin ƙwarewar yaren Turanci, Rukayya Fema mai shekaru 15 ta zama ta farko a gasa ta muhawara (debate), yayin da Hadiza Kalli ta lashe lambar yabo ta baiwa na musamman da kuma zinariyar lamba.

A cikin wata wasika zuwa ga ɗaliban, Ahmadu Shehu, sakataren riko na gidauniyar, ya ce tallafin karatun ya haɗa da ɗaukar nauyin karatun su har zuwa jami’ar da su ke so su je yin karatu.

Leave a Reply