No menu items!

Sample Page Title

Date:

Gwamnatin Najeriya ta shawarci ƴan ƙasar da ke zaune a Afirka ta Kudu kan su kula da kansu kafin da kuma bayan wasan da ƙasar za ta yi da Afirka ta Kudu a Gasar AFCON.

Ofishin jakadancin Najeriya da ke birnin Pretoria na Afirka ta Kudu ne ya fitar da wannan sanarwar inda ya ce ya kula da wasu maganganu da ake yi a shafukan sada zumunta waɗanda ka iya tayar da hargitsi bayan wasan.

“Galibin kalaman sun ƙunshi barazanar da ake yi wa “’ƴan Najeriya kan dafa dukar shinkafa” kafin wasan, da kuma “saka wa ƴan Nijeriya barkono idan Bafana Bafana ta sha kashi a hannun Super Eagles a ranar Laraba 7 ga watan Fabrairun 2024,” in ji sanarwar.

“Sakamakon haka, ofishin jakadancin ke bayar da shawara ga ƴan Najeriya da su lura da abubuwan da za su furta da kuma wurin da za su je kallon wasan musamman a bainar jama’a, da kuma guje wa ɗaga murya a lokacin murna ko tayar da rikici ko murna cikin tsokana idan Super Eagles ɗin ta yi nasara a wasan.

KU KUMA KARANTA: Dalilin da ya sa Ahmed Musa bai buga wasa ko ɗaya ba, a wasan cin kofin Afirka

“Haka kuma, ƴan Najeriya su ci gaba da nuna kyakkyawar ɗabi’ar da aka san su da ita, su kuma bi doka kafin da kuma bayan wasan. Ko da an harzuƙa, kada su mayar da martani, su kai koke wurin hukumomin da suka dace,” kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.

Duka wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke shirin buga wasan daf da ƙarshe da Afirka ta Kudu a Gasar AFCON a ranar Laraba.

A ɗayan ɓangaren kuwa Ivory Coast wadda ke karɓar baƙuncin gasar za ta fafata da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo a ranar Larabar.

Duk waɗanda suka yi nasara a cikin rukunan biyu za su fafata a wasan ƙarshe a ranar Lahadi 11 ga watan Fabrairun 2024.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...