Ganduje ba zai iya kallon idona kai tsaye ba, ni ubansa ne a siyasa – Kwankwaso

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ‘New Nigeria Peoples Party’ (NNPP) a zaɓen 2023, kuma tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, ya bayyana tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, a matsayin ɗansa na siyasa wanda ba ya iya haɗa ido dani kai tsaye.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani ga barazanar da Gwamna Ganduje ya yi masa na cewa zai mari shi idan ya haɗu da shi a fadar shugaban ƙasa a ranar Juma’a.

Kwankwaso da Ganduje sun je Villa ne a ranar Juma’a, kuma sun yi wa shugaban ƙasa Bola Tinubu bayanin abubuwan da ke faruwa a jihar Kano.

KU KUMA KARANTA: Zaɓaɓɓen Gwamnan Kano zai sake duba batun tsige Sanusi – Kwankwaso

Da yake magana da sashen Hausa na BBC a ranar Asabar, Kwankwaso ya ce tsohon gwamnan ya ruɗe lokacin da ya yi wannan tsokaci.

“Na ji shi (Ganduje) yana cewa zai mare ni, amma barazana ce ta fankan fayau.

Ya ruɗe kawai. Waɗannan duka yara na ne a siyasance. Ba zai ma iya kallona kai tsaye ba, idan muka haɗu.

A cikin ruɗani yake faɗin haka. Idan sun ganni sai su runtse idonsu,” inji shi.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar ya ƙara da cewa shugaban ƙasar ya kaɗu a lokacin da ya sanar da shi irin ta’asar da gwamnatin Ganduje ta tafka a Kano.

“Wasu mutane sun je sun yi masa ƙarya (Tinubu), amma da na bayyana masa gaskiyar lamarin, sai ya yi mamaki.

Ya yi mamakin yadda gwamna zai iya sayar da sashen jami’a, ya rushe shi, ya gina wa kansa fili”.

Ya kuma yi zargin cewa tsohon gwamnan ya sayar da filayen wasannin tsere na Kano, sansanin Hajji, da filin Idi ga ‘yan’uwansa da abokan arziƙi.

Da yake mayar da martani kan zargin cewa gwamnatin jihar ba ta bayar da isasshiyar sanarwa ba kafin a fara aikin rusau, Kwankwaso ya ce gwamna mai ci yana cika alƙawuran yaƙin neman zaɓe ne kawai.


Comments

2 responses to “Ganduje ba zai iya kallon idona kai tsaye ba, ni ubansa ne a siyasa – Kwankwaso”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Ganduje ba zai iya kallon idona kai tsaye ba, ni ubansa ne a siyasa – Kwankwaso […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Ganduje ba zai iya kallon idona kai tsaye ba, ni ubansa ne a siyasa – Kwankwaso […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *