Fiye da mutum miliyan bakwai ke kamuwa da cutar shanyewar ɓarin jiki duk shekara – Bincike

0
73
Fiye da mutum miliyan bakwai ke kamuwa da cutar shanyewar ɓarin jiki duk shekara - Bincike

Fiye da mutum miliyan bakwai ke kamuwa da cutar shanyewar ɓarin jiki duk shekara – Bincike

Daga Ibraheem El-Tafseer

Wani sabon bincike ya nuna ɗaya daga cikin babbar cutar da ke hallaka mutane wato shanyewar ɓarin jiki na ƙaruwa ne sanadin gurɓatacciyar iska da zafin jiki da matsananciyar ƙiba, da kuma hawan jini.

KU KUMA KARANTA:Ɓarkewar cutar mashaƙo ta halaka mutane 40 a Kano

Ƙididdigar ta baya-bayan nan ta nuna sama da mutum 7000 ne suka mutu, wasu sama da miliyan bakwai ke kamuwa da cutar a duk shekara, yayin da wasu da dama suka rasa wani sashe na jikinsu.

Sabon rahoton da mujallar kiwon lafiya ta The Lancet Neurology ta fitar, ta ce an samu ƙaruwar masu fama da cutar shanyewar ɓarin jiki da kashi 70 cikin 100 tsakanin shekarar 1991 zuwa 2021.

Leave a Reply