No menu items!

Sample Page Title

Date:

Fitacciyar mai gabatar da labarai a gidan talabijin na Najeriya (NTA), Aisha Bello, ta rasu.

Aisha, wadda ta shahara a NTA ta rasu da misalin karfe 9 na daren ranar Lahadi.

Duk da yake har yanzu babu cikakken bayani game da rasuwarta, amma ta yi aiki har ta kai matsayin manaja a NTA, kuma ta yi ritaya a watan Mayun 2022.

Rahotanni sun bayyana cewar za a yi jana’izar ta a babban masallacin ƙasa da ke Abuja, a yau.

Marigayiyar ta yi aiki tare da fitattun mutane kamar Cyril Stober, Eugenia Abu da dai sauransu.

An fi sanin ta a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu karanta labaran NTA na karfe 9 na dare a shekaru 20 da suka gabata.

A cikin wata sanarwa da ’yan uwanta suka fitar, sun bayyana cewar, “Innalillahi wa inna ilai raji’un. Allah Ya gafarta wa Hajiya Aishat Bello Mustapha, mahaifiyarmu.

“Lallai ke mutuniyar kirki ce Mama, lallai kina da kirki. Za mu yi kewar ki da fatan Allah Ya gafarta miki.”

Za a yi jana’izar da karfe misalin karfe 1 na rana a ranar Litinin.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...