Fitaccen ɗan wasan barkwanci na Najeriya, John Okafor, ya mutu     

0
149

Fitaccen ɗan wasan barkwanci na Najeriya, John Okafor, wanda aka fi sani da Mr Ibu, ya mutu yana da shekaru 62, kamar yadda Ƙungiyar Ƴan Wasan Kwaikwayo ta Najeriya ta tabbatar.

Mr Ibu ya rasu ne ranar Asabar a Asibitin Evercare da ke unguwar Lekki a birnin Lagos.

An garzaya da ɗan wasan kwaikwayon sashen bayar da kulawar gaggawa da rana, sai dai rai ya yi halinsa, in ji sanarwar da iyalansa suka fitar.

Shugaban Ƙungiyar Ƴan Wasan Kwaikwayo ta Nijeriya Emeka Rollas Ejezie, ya ce Mr Ibu ya mutu bayan ya yi fama da “bugun zuciya.”

KU KUMA KARANTA: Mutane 20 sun mutu a wani kwale-kwale da ya nutse a gaɓar tekun Senigal

Rollas, wanda ya tabbatar da rasuwar Mr Ibu a shafinsa na Instagram, ya ƙara da cewa Don Single Nwuzor, manajan da ya kwashe shekaru 24 yana aiki tare da Mr Ibu ne ya gaya masa rasuwar ɗan wasan kwaikwayon.

A watan Nuwamban 2023 ne aka yanke ɗaya daga cikin ƙafafun Mr Ibu sakamakon larurar da yake fama da ita a wancan lokacin.

A watan Disamba kuma, iyalan ɗan wasan kwaikwayon suka fitar da sanarwar da ke musanta cewa an yanke masa ƙafa ne sakamakon ciwon suga.

Leave a Reply